Ahmad Salkida shahararren danjaridar nan dake samun labarai daga shugabannin kungiyar Boko Haram ya ce 15 ne kacal suke a raye daga cikin yan matan Chibok 113 dake tsare a hannun Boko Haram.
Salkida wanda ya bayyana haka cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce da yawa daga cikin yan matan sun mutu sakamakon musayar wuta tsakanin sojoji da yayan kungiyar ta Boko Haram a lokacin da sojojin suka yi kokarin ceto su.
Yau shekara hudu kenan tun bayan da aka sace yan matan su 276 daga makarantar sakandaren yan mata dake Chibok a jihar Borno.
Ya yin da 163 suka dawo hannun iyayensu an yi ittifakin cewa ragowar yan matan 113 na can tsare a hannun Boko Haram.
Amma Salkida ya ce ragowar yan matan da suke a raye basa hannun shugaban kungiyar, Abubakar Shekau.
A cewarsa an aurar da su inda ya ce mazajensu ne kawai za su iya yanke makomarsu.
Ya kara da cewa tattaunawa ko kuma biyan kudin fansa ba zai sa a saki yan matan ba sai dai idan har mazajensu sun sake su.