Wasu Yan Mata ‘yan kimanin Shekaru 14 Sun kirkiro hanyar amfani da fitsari a maimakon fetur a cikin injin janareto.
Yan Matan guda hudu masu sunaye Duro-Aina Adebola, Akindele Abiola, Faleke Oluwatoyin, da Bello Eniola Sun samu nasarar kirkirar hanyar amfani da fitsarin dan adam a maimakon man fetur. A jawabin su, yan matan sunce, lita daya ta fitsari zai dauki janareto tsawon awa shidda yana aiki.
Sun kara da cewa, a cikin fitsari akwai sinadarin ammonia, inda Sabuwar hanyar tasu take tace sinadarin Hydrogen dake cikin ammonia domin saka janareto yayi aiki.