‘Yan Matan Chibok 100 Sun Zabi Zama Da BokoHaram Akan Gidan Iyayensu. 


Wasu rahotanni daga BBC HAUSA na cewa fiye da ‘yan matan Chibok dari daya da ke hannun ‘yan Boko Haram sun fi son zama a hannun mayakan maimakon dawowa wurin iyayensu.
Shugaban kungiyar cigaban al’ummar Chibok, Mr Pogba Bitrus, wanda ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labarai na AP, ya ce yana ganin ‘yan Boko Haram sun sauya tunanin ‘ya’yan nasu ne. Ko kuma a cewarsa, ‘yan matan suna jin kunyar dawowa gida saboda gudun yadda jama’a za su rika kallonsu, ko kuma su fuskanci tsangwama

You may also like