Yan Najeriya 198 Da Gwamnatin Saudiya Ta Koro Sun Sauka A Filin Jirgin Sama Dake Kano Gwamnatin tarayya a ranar Asabar ta karbi yan Najeriya mutane 198 dake zaune a kasar Saudiya ba bisa kaida ba,mutanen sun sauka a filin jiragen sama na Mallam Aminu Kano dake Kano da misalin karfe 10:00 na safe. 

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, ya rawaito cewa wannan wani kasone na yan Najeriya su  1,800 da ke zaune a Saudiya ba bisa kaida ba. aka kuma yi musu afuwa kan su koma kasashen su. 

NAN ya rawaito cewa mutanen su 198 da suka hada da mata da kananan yara sun dawo tare da jakunkunan kayansu a cikin jirgin sama mallakar kamfanin Med View.

Jami’an hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA sune suka karbi kason farko na mutanen dake dawowar.

Muhammad Yahaya Sani Jami’i a Ofishin jakadancin Najeriya dake Jeedda, wanda ya jagoranci masu zaman cirani zuwa Najeriya ya shaidawa yan jaridu a filin jirgin cewa gwamnatin tarayya ce ta dauki nauyin dawo da mutanen gida. 

A cewarsa mutanen ne da kansu suka kai kansu ofishin jakadancin Najeriya dake Jeedda domin su dawo gida bisa bin dokar afuwar da gwamnatin kasar Saudiya tayi  kan su fice daga kasar kafin wa’adin ranar 24 ga watan Yuli da ta basu ya cika. 

Yahaya Sani yace  ba kamar yadda mutane suke yadawa ba,mutanen ba korosu akayi ba, sun karbi tayin afuwar da gwamnatin Saudiya tayi kan duk wanda ke zaune a kasar ba bisa ka’ida ba to ya bar kasar. 

” Sun yanke shawarar dawowa gida Najeriya a kashin kansu,gwamnatin Saudiya ce tayi afuwa ga duk wadanda suke zaune a kasar ba bisa ka’ida kan su fice daga kasar cikin watanni uku, ” yace. 

Jami’in ya damka wadanda suka dawo a hannun hukumar NEMA dake filin jirgin wadanda suka ga yadda aka tantance mutanen kafin daga bisani kowannensu ya tafi garin da yafito.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like