‘Yan Najeriya mazauna Amurka zasu habaka tallafin arzikin kasar


‘Yan Najeriya mazauna kasar Amurka sun ce a shirye suke su zuba jari domin habaka tattalin arzikin kasar muddin gwamnati zata samar da kaykkyawan tsarin da zai basu damar yin hakan.
‘Yan Najeriyar sun bada wannan tabbaci a lokacin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yake ganawa da su a birnin New York a yau Juma’a.

Taron dai ya maida hankali kan tattauna yadda kwararrun ‘yan Najeriyar zasu bada gudunmawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasar.

An dai gudanar da wannan taro a daidai lokacin da ake taron Majalisar Dinkin Duniya kashi na 71 a birnin na New York da ke Amurka.

You may also like