‘Yan Najeriya Mazauna Nijar Sun bayyana Damuwa Kan Fara Hako Mai A Arewacin NajeriyaAGADEZ, NIGER – ‘Yan kasar da ke Nijar sun bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da suka fitar, inda suka bukaci gwamnatin Najeriya ta dauki matakin da ya da ce.

Watanni kusan biyar da shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya kaddamar da hakar man fetur a Kalmoni da ke kan iyakokin jihohin Bauchi da Gombe a arewa maso gabashin kasar, Buhari ya sake kaddamar da aikin hakar mai a karamar hukumar Obi da ke jihar Nasarawa, abin da ya sa ake da man a wurare biyu a arewacin kasar yanzu.

Yayin da mutanen yankin ke murna game da hako mai a arewacin kasar wasu kuma fargaba suke, duba da abin da ke faruwa a yankin Naija Delta, kamar matsalar gurbatar muhalli da kuma ayyukan masu fasa bututun mai.

Malan Lawan Ahmed, ‘dan asalin yankin arewacin Najeriya ne kuma mamba a kungiyar ‘yan Najeriya mazauna Nijar, ya ce duk inda aka ce za a soma hako man fetur akan samu fitintunu da ke biyo baya, to amma ya kamata gwamnati ta kafa wata hukuma da zata sanya ido sosai don gudun faruwar hakan.

Tunda aka kaddamar da soma hako man fetur a yankin arewa maso gabashin Najeriya ‘yan yankin suka fara murnar cewa wannan wata dama ce ta bunkasa tattalin arzikin yankin da ma kasar baki daya, to sai dai Malam Ibrahim Siraji na ganin samar da daidaito a tsakanin al’ummomin kasar zai taimaka wajen kawar da duk wani fargaba da mutanen arewa ke da shi.

Bayan shafe shekaru ana hakar man fetur a yankin Naija Delta al’umar yankin suke kokawa kan rashin amfana da alherin man da ake hakowa, to sai dai ‘yan arewacin Najeriya na ganin samar wa matasa aiki zai kawar da duk wata fargaba.

Malam Isyaku Abdullahi, ya ce ya kamata mutanen arewacin Najeriya su guji sakacin da ka iya sa su guje wa aiki saboda tunanin cewa an samu arzikin man fetur a garinsu.

Ma’adana na ganin abin da ya kamata mutanen arewacin Najeriya su yi shi ne su sanya mutanen da ake hako man a yankunansu, kafa wani kwamiti na amintattu da zasu rinka kula da yadda ake sarrafa kudin.

Saurari cikakken rahoto daga Hamid MahmudSource link


Like it? Share with your friends!

-1

You may also like