Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar yayi zargin cewa kusan yan Najeriya miliyan 3 ne suka gwamnatin jam’iyar APC ta raba da aiyukansu.
Atiku ya bayyana haka a ranar Asabar lokacin da yake bayyana komawarsa jam’iyar PDP.
Tsohon mataimakin shugaban kasar wanda ya fice daga jam’iyar APC a watan Nuwamba yace ya shigar jam’iyar ne saboda yana ganin zata kyautata rayuwar yan Najeriya.
Ya ce ” Naji daɗi kan alkawarin jam’iyar na samar da aiyukan yi miliyan 3 a cikin shekara ɗaya.”
“Amma sakamakon ba shi ne wanda aka yiwa mutane alkawari ba a cikin shekara biyu kusan yan Najeriya miliyan 3 ne suka rasa aikinsu.”