‘Yan Najeriya Na Ci  Gaba Da Yi Wa Kasa Addu’a A Kasa Mai Tsarki Wasu ‘yan Nijeriya da yanzu haka suke gudanar da aikin Umrah na ibada a kasa mai tsarki na ci gaba da yiwa kasar Nijeriya addu’a don neman samun sauki ga matsalolinta musanman ‘yan kasar da kuma neman samun sauki ga rage matsalolin radadin talauci da yanzu haka yake yiwa mafi rinjayen yan kasa masu karamin karfi illa.
Alhaji Yusuf Dingyadi, Sakataren Watsa Labarai na Jam’iyyar PDP a Jahar Sokoto kuma daya daga cikin shugabanin Kungiyar Ciyar Da Arewa Gaba (Arewa Development Forum) da yanzu haka ya je garin Madina kan hanyarsa ta zuwa Makkah yace, hakika ala dole kowane dan kasa ya zauna ya yi wa kansa karatun ta natsu sakamakon yadda matsalolin suke ta karuwa a cikin mafi rinjayen al’umma da sanya su a cikin wasu wahaloli da rashin ingantaccen tsari na ciyar da kasa gaba da ceto ta daga wannan yanayi.
Alhaji Yusuf Dingyadi ya baiyana cewar, wasu daga cikin shugabanin da aka dora ma alhakin baiwa jama’a jagoranci a cikin al’umma sun kasa tare da kirkiro wasu manufofi maras amfani ga yanayin da inganta rayuwar mai karamin hali, abin da ya kara janyo masa matsala ga rayuwarsa; wannan abin dai yana kara janyo wahala iri iri a cikin kasa.
“Matsalar tsaro, talauci, rashin aikin yi da yawan tashe tashen hankula na rashin tabbas ga kasa da lallacewar tattalin arziki ya zama wani abin tunani don lamuran sun yi yawa a kasarmu, don haka dole mu zauna damu da sauran jama’ar dake anan kasa mai tsarki mu yiwa kasa addu’a tare da fatan samun fita daga wannan yanayi, a matsayinmu na yan Najeriya” inji Dingyadi.
Sakamakon haka ya bukaci gwamnatin tarayya da na jihohi dasu fitar da hanya da ta dace ga inganta rayuwar al’ummma.

You may also like