‘Yan Najeriya na kokawa kan karancin sababbin takardun kudin da gwamnati ta kaddamar



new naira banknotes

Kwanaki 17 bayan da aka fitar da sabbin takardun kudin Najeriya, na Naira 200 da 500 da kuma 1, 000 da babban bankin kasar, ya yi,
yawancin ‘yan kasar na cewa har yanzu ba su taba ganin sabon kudin ba ballantana ma su rike.



Da dama daga cikin ‘yan kasar sun nuna damuwarsu dagane da yadda sabon kudin ke wahala, ko a bankuna da wuraren cirar kudi na ATM. 



Jama’a na nuna damuwar ne yayin da ya rage kasa da kwana 28 a daina amfani da tsoffin takardun kamar yadda babban bankin kasar ya sanar a kwanakin baya. 



Wakilin BBC ya ziyarci wasu gundumomin da ke kwaryar birnin Abuja, inda ya tambayi wasu ‘yan kasar bin da suka fahimta daga karancin sababbin takardun kudin.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like