‘Yan Najeriya Suna Da-Na-Sanin Rashin Sake Zaben PDP –  Makarfi



Shugaban Riko na bangaren jam’iyyar PDP, Sanata Ahmed Mohammed Makarfi ya bayyana cewa mafi yawan ‘yan Nijieriya sun yi da-na-sani kan matakin da suka dauka na kin sake zaben PDP a lokacin zaben shekarar 2015.
Makarfi ya yi wannan ikirarin ne a lokacin da yake karbar rahoton sakewa jam’iyyar fasali daga hannun tsohon Ministan Yada Labarai, Farfesa Jerry Gana inda ya nuna cewa a shekarar 2019, PDP za ta sake kafa gwamnatin tarayya idan har ‘ya’yan jam’iyyar suka taka rawar da ta dace a yayin zaben.

You may also like