
BBC ba za ta bayyana bayanan Mohammed, da ke neman mafaka ɗan Rwanda
Ina fafutuka ne kawai don na rayu “wani mutum da ke magana cikin rawar murya, kuma cike da tsoro,” ya faɗa.
Muna tsaye ne a Wasteland da ke babban birnin Kigali cikin ƙasar Rwanda.
Wurin, yana zagaye da bishiyoyi don ba mu mafaka daga idanun masu farauta.
Muhammad ya zo ƙasar nan ne don samun mafaka. Ya gudo daga yankin Rwanta na Ethopia, inda yake gudun hijira, har zuwa lokacin da wakilan kasarsa suka yi yunƙurin ɗauke shi.
Mohammed ya ce rayuwa a Kigali akwai wuya, yana tsoron martani da ka iya tasowa idan ya yi magana da ‘yan jarida, hakan ta sa ya nemi mu sakaya sunansa da garinsu na gaskiya, sai dai mu ce a Afirka yake kawai.
Tsawon kwanaki muna ta ƙoƙarin samun masu neman mafaka da ke zaune a Rwanda don yin magana da su.
A lokuta daban-daban mutane kan amsa, ciki wani abu mai ɗaure kai, sai a neme su a rasa, musamman bayan ziyarar da shugabanin unguwanninsu suke kai musu”.
“Na nemi a ba ni mafaka,” Muhammad yake fada min.
“Hukumomin ba sa cewa ‘a’a, amma komai sai dai su ce na dawo ‘gobe’ ko ‘ku dawo watan gobe’. An kai shekara ɗaya yanzu amma har zuwa yau ba su ba ni ba.
‘Tilas na yi magana da Mohammed, yayin da babbar kotun da ke Burtaniya take duba halaccin shirin gwamnatin ƙasarr mai cike da taƙaddama, na tura wasu daga cikin masu neman mafaka zuwa Rwanda.
A Ranar Litinin, alƙalin ya yanke hukuncin kan matakin inda ya ce manufar gwamnatin daidai ce, a mayar da su ƙasarsu, amma sai dai mayar da su ɗin zai tafi ne cikin “tsarin Majalisar Dinkin Duniya, kan ‘yan gudun hijira, duk da bukatar takwas daga cikin masu neman mafakar har yanzu ba a amince da ita yadda ya kamata ba.
Gwamnatin ta Burtaniya ta amince cewar jadawalin mayar da ‘yan Rwanda da ke neman mafaka kasar gida, hakan ka iya zama gargaɗi ga masu ƙoƙarin zuwa kasar a cikin kananan jiragen ruwa.
Amma masu adawa na cewar manufar ta yi tsauri, kuma babu wani tasiri da za ta yi.
A kwanaki, kungiyar rajin kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch (HRW) ta bayyana damuwarta kan halin da ake ciki a Rwanda, suna cewa ‘tauye ‘yancin fadar albarkacin baki ne, da tsare mutane ba bisa ka’ida ba, ga kuma azabtarwa’.
A wani bincike da aka wallafa a farkon shekarar nan, gwamnatin Burtaniya ta ce “duk da yake akwai take hakkin dan adam” ba a saba gani ba mutumin da aka mayar da shi gida daga Burtaniya ya fuskanci rashin adalci.
Asalin hoton, Getty Images
Shirin mayar da masu neman Mafaka Rwanda ya haifar da sarkakiya a Burtaniya
Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ya fadawa kotun cewar Rwanda ba ta da ‘mafi karanci abubuwan da ake bukata, da za a iya dogaro da su, ba tare da nuna bambanci ba, a tsarin masu neman mafaka.’
Ta damu cewar za a mayar da mutane kasashensu inda suke fuskantar azabtarwa.
Haka Kuma wani rahoton hukumar ta MDD ya ce “hanzari da matakan da ake bi, abin damuwa ne, saboda yadda matakan kan dauki shekara daya zuwa biyu, a wasu lokutan.
Mohammed ya ce yakan ji rayuwarsa ta shiga mawuyacin hali, ba ya iya yin halattaccen aiki, saboda ba shi da takardu.
“Abokai da dangi na taimakawa,” ya ce, yakan samu ‘yan kudade daga kananan ayyukan da yake yi.
Amma ga mutum mai mata da ‘ya’ya, rashin tabbas din na da yawa.
Ya ce yana son ya bar Rwanda, ya je wani wuri mai cike da zaman lafiya, kamar Candako a Australia”.
Cikin damuwa da kungiyoyin da ke adawa da shirin Burtaniya na mayar da masu neman mafakar, shi ne makomar yan kungiyar ‘yan luwaɗi da maɗigo ta LGBT a Rwanda.
Saɓanin wasu kasashe da ke makwabtaka da ita, luwadi ba laifi ba ne a Rwanda .
Amma wata budaddiyar wasika da aka rubutawa HRW, ta ce ‘yan maɗigo, da ‘yan luwadi, da masu jirkita halitta na fuskantar tsangwama.
A 2021, a wani ajiyayyen jawabi kan yadda hukumomi ke cin zarafi, tsarewa ba bisa ƙa’ida ba, zagi da cin zarafi” wasu masu jirkita halitta da ‘yan luwaɗi 9, a Cibiyar Gikondo Transit da ke Kigali, a wani haramtacen wurin tsare mutane, a cewar HRW.
Asalin hoton, Getty Images
HRW ta kalubalanci cibiyar Gikondo Transit da ke babban birnin Rwanda, kamar yadda aka nuna a hoton dake sama
“Wadanda aka tattauna da su sun ce an kai musu hari saboda neman jinsi da suke, ko bayyana jinsin da suke, kuma su kan fuskancin hukunci mai tsauri fiye da sauran wadan ake tsare da su.
‘Yan sandan ko masu gadin kan zarge su ne rashin matsuguni, barayi, inda suke ajiye su a dakin da aka ajiyewa masu aikata manyan laifuka, a cewar kungiyar.
Daya daga cikin mutanen da suka fahimci cusgunawar da ‘yan luwadi ke fuskanta a Rwanda shi ne Patrick Uwayezu.
Dan luwadin majami’ar Evangelical ta Afirka a Rwanda, daya tilo a Kigali da ke maraba da Ayykan yan kungiyar neman jinsi.
Siririn mutum dake da karfin muryar waka, yana jagorantar mawakan majami’a da muke zuwa a ranar Lahadi.
Daga bisani ya sanar da ni cewar ‘yan kungiyar LGBT, kan sha wuya, wajen samun kulawa a fanin lafiya saboda yadda ake tsangwamarsu.
“idan ka boye ko waye kai, za su iya baka aikin yi. amma idan ma’aikata suka gano ko kai waye zasu fada maka cewar maza ka tafi, ba zasu iya aiki da kai ba.”
“Ina mutane masu yawa basu fahimce mu ba a cikin kasar nan,” a cewarsa.
Asalin hoton, Getty Images
Patrick Uwayezu ya ce yan kungiyar LGBT, sun ce su kan sha wuya kafin su sami kulawa a harkokin lafiya
Asalin hoton, Getty Images
Teklay Teame came to Rwanda from Eritrea in 1998