Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya ce alamu sun gama bayyana cewa yan Nigeria a yanzu babu abunda suke kewa kamar jam’iyyar PDP ta karbi mulkin kasarnan a 2019.
Mista Jonathan yace yan Nigeria na kaunar jam’iyyar PDP a shirye suke kuma su fito kwai da kwarkwatansu su zabe ta a shekarar 2019.
Tsohon shugaban kasar ya bayyana haka ne a yayin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da sukayi a hedikwatar jam’iyyar a Abuja
Majiyarmu ta ruwaito tsohon shugaban kasar a don haka ya shawarci ‘yayan jam’iyyar da su hadu su dunkule domin kaiwa ga nasara
Yace hadin kan jam’iyyar shine zai bawa yan baruwana da sauran ragowar ‘yayan jam’iyyar da suka fice su dawo
ME ZAKU CE?