‘Yan Nijeriya Sun Fara Kalubalantar ‘Yan Majalisa Dake Karbar Albashi Da Fansho a Lokaci Daya


 

Wasu ‘yan Nijeriya sun farga akan yadda wasu da yawa daga cikin ‘yan majalisu da ministocin Nijeriya wadanda suka rike mukaman gwamnati a baya ke karbar albashi biyu a kowanne wata da ya kunshi fansho daga mukamin su na da da kuma albashinsu na ‘yan majalisa.

Akalla tsoffi gwamnoni da mataiakansu guda 21 ne a yanu haka ke rike da mukaman ‘yan majalisu, inda a cikinsu, wadanda suka yi ayyukan gwamnati ko kuma aikin Soja kafin su rike mukaman gwamnati ma ke karbar fansho biyu da kuma albashin su na ‘yan majalisa.

A karkashin dokar Nijeriya, ba a yarda wani wanda ke rike da mukamin gwamnati ba ya karbi wani biya na mukamin da ya rike a baya, sai dai wannan doka ta cire ‘yan majalisa daga wannan sahu, dalili kuwa bai wuce cewa su suka kafa dokar ba.

‘Yan Nijeriyan da suka tofa albarkacin bakin su sun kira al’amarin cuta da zalunci, rashin tausayi da rashin sanin ya kamata.

A wani bincike da jaridar Vanguard ta yi ta gano cewa kimanin tsoffin gwamnoni 47 daga jahohi 21 kawai a yanzu haka na samun biliyan 47 daga asusun gwamnati.

Rahotanni na nuna cewa tsofffin gwamnoni na samun sabbin motoci 3 zuwa 6 a kowanne shekaru 4, su na samun ninki uku na albashin su a matsayin alawus din gyaran gida a kowanne shekaru biyu, su na samun tsakani miliyan 30 zuwa miliyan 200 a matsayin fansho a duk shekara da sauran alawus alawus, duk da cewa su na karbar albashin su da alawus din su na kasancewa ‘yan majalisa.

Shugaban majalisar Bukola Saraki yayin da yake mayarda martani akan kalubalantar su da aka yi, ya ce suna karbar wadannan kudade ne kamar yadda dokar kasa ta tanadar.

Tsoffin gwamnonin da yanzu haka suke rike da mukaman ministoci a gwamnatin Buhari sun hada da Rotimi Amaechi (Rivers), Chris Ngige (Anambra), Kayode Fayemi (Ekiti), da Babatunde Fashola (Lagos).

Tsoffin gwamnonin da suke rike da mukaman sanatoci a yazu haka sun hada da: Bukola Saraki (Kwara), Rabiu Musa Kwankwaso (Kano), Kabiru Gaya (Kano), Abdullahi Adamu (Nasarawa), Godswill Akpabio (Akwa Ibom),  Sam Egwu (Ebonyi), Shaaba Lafiagi (Kwara), Joshua Dariye (Plateau) Theodore Orji (Abia), da Jonah Jang (Plateau).

Sauran sun hada da: Aliyu Magatakarda Wamakko (Sokoto), Ahmed Yarima (Zamfara), Danjuma Goje (Gombe), George Akume (Benue), Bukar Abba Ibrahim (Yobe), Adamu Aliero (Kebbi), da Isiaka Adeleke (Osun).

Tsoffin mataimakan gwamnoni a majalisar sun hada da Biodun Olujimi (Ekiti) da Enyinaya Harcourt Abaribe (Abia), sai kuma Sanata Danladi Abubakar Sani wanda ya rike mukamin gwamna na riko a jahar Taraba

‘Yan Nijeriya da dama dai na kira da a gyara wannan doka da ta sanya wasu ‘yan tsirarun mutane suna tatse asusun gwamnati duk da cewa kasar na cikin wani hali.

You may also like