‘Yan Nijeriya Sun Rage Ciki a Sakamakon Matsin Tattalin Arziki – Bincike


food-shortage

Wani sabon bincike da kamfanin NOIPolls ya gudanar a jiya Laraba ya bayyana cewa matsin tattalin arzikin da kasar ke ciki ya sanya masu iyali rage yawa da kuma sauya irin abincin da suke ci yayin da wasu kuma suka koma ga Allah wajen yawaita addu’oin samun sauyi.

Binciken wanda kamfanin ya gudanar tare da hadin gwiwar ‘Business Day Media’ ya bayyana cewa kusan kaso 2 cikin 3 na mutane miliyan 170 da ke Nijeriya sun koka da yanayin ha’ula’i da su da iyalansu suka shiga tun lokacin da tattalin arzikin kasar ya fara tabarbarewa kusan watanni uku da suka wuce.

Haka kuma binciken ya bayyanawa ra’ayoyin ‘yan Nijeriyan game da dalilan faruwar hakan inda da yawa daga cikin wadanda aka tambaya suke ganin cewa sauye sauye da aka samu a tsarin tattalin arzikin kasar (Misali raguwar kudaden shigar gwamnati a sakamakon faduwar farashin man fetur a kasuwar duniya) shi ya haddasa al’amarin.

Manya daga cikin matsalolin da ‘yan Nijeriya ke fuskanta a wannan lokaci sun hada da karin farashin kayan masarufi, Karin farashin man fetur, karin farashin kudin zuwa da zawwa, faduwar darajar Naira, raguwar samun wutar lantarki yayin da farashinsa ya karu, da sauransu.

Rahoton binciken ya nuna cewa akwai abubuwa da dama da ‘yan Nijeriya ke yi wajen rage zafin wannan yanayi wadanda suka kunshi rage amfani da kayan walwala da jin dadi, addu’oi, rage yanayin abinci da yawan abincin da ake ci, samun wasu hanyoyin daban na samun kudi da kuma yin noma.

Cc: Alummata

You may also like