
Asalin hoton, Getty Images
‘Yan wasan Real Madrid 13 aka gayyata tawagoginsu, domin buga wa kasashensu tamaula a makon nan da na gobe.
A cikin makon nan za a buga wasannin neman gurbin shiga gasar nahiyar Turai da na Afirka da kuma wasannin sada zumunta.
Wadanda aka gayyata sun hada da Carvajal da Nacho da kuma Ceballos daga Sifaniya, Courtois daga Belgium, Camavinga da Tchouameni daga Faransa.
Wasannin da za a buga a makon nan da na gobe
- Spain da Norway ranar Asabar 25 ga watan Maris
- Scotland da Spain Talata 28 ga watan Maris
Kociyan tawagar Sifaniya ya gayyaci Carvajal da Nacho da kuma Ceballos, domin buga fafatawar neman shiga Euro 2024.
- Sweden da Belgium Juma’a 24 ga watan Maris
- Jamus da Belgium Talata 28 ga watan Maris
Courtois zai buga wa Belgium wasan shiga European Championship rukuni na shida ranar Juma’ a da Sweden kwana hudu tsakani da Jamus a wasan sada zumunta.
- Faransa da Netherlands Juma’a 24 ga watan Maris
- Ireland da Faransa ranar Litinin 27 ga watan Maris
Camavinga da Tchouameni za su buga wa Faransa wasannin shiga UEFA EURO 2024 da za ta kara da Netherlands a Faransa da kuma Ireland a Dublin Arena.
- Croatia da Wales Asabar 25 ga watan Maris
- Turkey da Croatia Talata 28 ga watan Maris
Luka Modrić zai yi wa Croatia wasannin neman gurbin shiga European Championship a fafatawa da Wales ta ziyarci Turkey.
Akwai karin bayanai……