Yan Sanda A Ebonyi Sun Tabbatar Da Kisan Da Wasu Yan Fashi Su Ka Yi Wa Wani Dalibin Jami’a


Rundunar yan sandan jihar Ebonyi ta tabbatar da cewa Chinedu  Linus dalibi a jami’ar  jihar Ebonyi dake Abakaliki,  yan bindiga sun kashe shi a ranar Juma’a.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, ASP loveth  Oja ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN cewa yan bindigar sun yi wa Linus fashi kafin daga bisani su harbeshi.

Odah tace har yanzu ba a kama kowaba kan lamarin amma rundunar tuni ta shiga farautar yan fashin.

” Ina shawartar dalibai da kada suyi jarumtar tunkarar yan fashin dake dauke da makami a duk lokacin da suka kai musu hari saboda irin wadannan mutanen ba a cikin hayyacinsu suke ba.

“Mutumin da yake a raye shine kawai za iya amfani da kayan da yake dashi saboda babu wani abu da mutum yake dashi darajarsa takai ran dan adam,”tace.

Mai magana da yawun rundunar tayi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su samar da titi zuwa dakin kwanan daliban domin jami’an tsaro su samu damar kai daukin gaggawa a duk lokacin da aka kaiwa daliban hari.

“Ma’aikatan mu sai da suka ajiye motar su akan titi inda suka taka da kafarsu har zuwa dakin kwanan daliban kafin su dauko gawar dalibin inda suka kai ta dakin ajiye gawarwaki na asibitin gwamnatin tarayya dake Abakaliki.”

You may also like