Yan Sanda A Jihar Kano Sun Kama Barayin Babura Su 17 


Rundunar yan sandan jihar Kano ta kama wasu mutane 17 da ake zargi da laifin kai hari da kuma kwacewa  masu babura mai kafa uku wanda akafi sani da Adaidaita sahu babur dinsu. 

Kakakin rundunar yan sandan jihar , Magaji Musa Majiya ya bayyana haka lokacin da yake nuna masu laifin ga manema labarai. 

Yace an kama mutanen ne bayan da rundunar ta gudanar da wani atisaye na musamman da aka yiwa lakabi da  ‘Shege Kafasa’ a yankunan da masu babur mai kafa uku suka fi yawa a cikin birnin. 

” Sakamakon wannan atisaye a unguwannin, Unguwa uku, Hausawa Gidan Zoo, Gyadi-Gyadi da kuma Bello Road, mun samu nasarar kama wasu mutanen da ake zargi.”

Yace  cikin wadanda aka kama har da wani kasurgumin barawo wanda ake zargi da sace babura sama da guda 100 a makarantu, asibitoci, da kuma manyan makarantu dake jihar. 

“Wannan kasurgumin barawon baburan yana amfani da Master Key da kuma wasu kayayyaki wajen aikata mummunan ta’asar da yake, ya zuwa yanzu ya saci babura sun kai 100.”

Kakakin rundunar yace yawancin wadanda aka kama sun dade suna kaiwa masu Adaidaita sahu hari da mugayen makamai,kafin su kwace musu babur da kuma wayoyin hannu da sauran kayayyakin fasinjojinsu.

Majiya yace za’a  cigaba da gudanar da atisayen domin raba jihar da bata gari,wadanda suke addabar mutanen jihar a yan kwanakin nan.

Yace kwamishinan yan sandan jihar Rabiu Yusuf, ya bawa Shugabannin yan sanda na yankuna umarnin  cigaba da sintiri a yankin. 

 

You may also like