Rundunar ‘Yan sandan jihar Kano ta zargi magoya bayan akidar Kwankwasiyya da haddasa rikicin siyasa a jihar wanda ya yi sanadiyyar mutane da dama suka samu raunuka a makon da ya gabata.
Kwamishinan ‘Yan sandan jihar, Rabi’u Yusuf ya ce magoya bayan Kwankwasiyya daga jihohin Sokoto, Kogi da wasu makwaftan jihohi sun yi wani gangami a Asibitin Hasiya Bayero da nufin tarwatsa Hawan Daushe wanda masarautar Kano ke shirya a duk shekara, lamarin da ya janyo arangama da magoya bayan Gwamnan Jihar, Umar Ganduje.