Yan Sanda A Jihar Ondo Sun Sake Kama Wani Dan Kungiyar Boko Haram


Muhammad Basha, da ake zargi da kasancewa dan kungiyar Boko Haram an kama shi a karamar hukumar Akoko ta Gabas dake jihar Ondo. 

Hakan na zuwa ne kwanaki shida bayan da aka kama Ibrahim Idris Abawo,wanda akafi sani da,Idiko dake cikin jerin sunayen yan kungiyar Boko Haram da ake nema ruwa a jallo.

Femi  Joseph mai magana da yawun rundunar yan sanda ta jihar yace an kama Basha ne lokacin da yake garari akan titin Isua-Ifira Akoko.

” Lokacin da aka kama mutumin da ake zargin ya amince da cewa shi dan kungiyar Boko Haram ne, mahaifinsa dan kasar Nijer ne yayin da mahaifiyarsa kuma yar Maiduguri ce babban birnin jihar Borno,” yace.

“Ya kuma ce wani mutum da ake kira Daffo shine shugaban rukuninsu yayin da shekau kuma yake shugaban kungiyar ga baki daya.”

Joseph yace kayayyakin da aka samu daga wurinsa sun hada da layu.ya kuma kara da cewa mai laifin yana hannun rundunar domin tatsar karin bayanai.

You may also like