Yan Sanda A Kano Sun Kama Mai Safarar Miyagun Kwayoyi Daga Lagos Da Darajarsu Takai Miliyan 17


Hoto:Daily Trust

Rundunar yan sandan jihar Kano ta kama wani matashi mai shekaru 22, Stanley Arinze kan zargin safarar miyagun kwayoyi nau’in Tramdol daga jihar Lagos zuwa Kano da darajarta takai naira miliyan 17.

Mai magana da yawun rundunar Magaji Musa majiya ya bayyana haka lokacin da yake ganawa da manema labarai ranar Talata a Kano. 

Yace an kama mutumin da ake zargi ranar 16 ga watan Yuli. 

” Arinze dan asalin jihar Anambra wanda ke zaune a Unguwar Jaba, yana hannun yan sanda bisa laifin safarar miyagun kwayoyi nau’in Tramdol katan 25 daga Lagos zuwa Kano da darajarsu takai miliyan 17.

Yace an boye kwayoyin ne cikin kwayayen talabijin din Plasma domin kan kaucewa jami’an tsaro.

” Mutumin da ake zargi ya wuce  shingayen binciken jami’an tsaro daga jihar Lagos, amma jami’an yan sanda masu saido suka tsayar da babbar motar a titin Bye Pass,” yace. 

Mai magana da yawun rundunar yace wanda ake zargin ya amince da aikata laifin kuma tuni rundunar ta shiga binciko abokan safarar tasa.  

You may also like