Yan Sanda  A Zaria Sun Kama Wanda Yayi Garkuwa Da Wani Injiniya Dan Kasar China 


Yan sanda sun kama daya daga cikin mutanen da sukayi garkuwa da wani Injiniya dan kasar China dake aiki a kamfanin dake aikin samar da ruwa a garin Zaria.

 Zhang Lijun wanda yake aiki da kamfanin gine-gine na CGC an sace shine a ranar Litinin a kauyen Dakace dake wajen Zaria  akan hanyar Jos, lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa wajen aiki.

 Da yake tabbatar da kama mutumin kakakin rundunar yan sandan jihar Kaduna, ASP Yakubu Sabo yace yan sanda sun samu nasarar ceto mutumin tare da kwato wasu kayayyaki daga wadanda ake zargi da garkuwa da shi. 

Saboda haka yayi kira ga maigidanta da su cigaba da taimakawa yan sanda da bayanai daza su taimaka wajen maganin garkuwa da mutane da kuma sauran laifuka a jihar.

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta fadawa jaridar Daily Trust yadda aka yi garkuwa da Liju “Yana tare da direbansa,Haruna Muhammad lokacin da wasu mutane biyu suka kai musu hari da bindiga, suka jefar da direbansa da sukayi awon gaba da Lijun,” a cewar majiyar.

 Mutumin da ake zargi da garkuwar  Paul Ochalla daga jihar Rivers da kuma daya mutumin daga jihar Akwa Ibom wanda ake nema, sun yi kokarin guduwa da mutumin amma basu yi nasara ba.

You may also like