Yan Sanda Hudu Sun Rasa Rayukansu A Wani Hari Da Ake Zargin Fulani Da Kaiwa Wasu mutane da ake zargin Fulani makiyaya ne sun kai hari kan motar yan sanda a Abraka, karamar hukumar Ethiope ta gabas, dake jihar Delta a ranar Talata inda suka kashe yan sanda hudu. 

Yan sandan, suna kan hanyarsu ta dawo wa daga kwantar da rikicin kan iyaka, tsakanin al’umomin Eka da Oria, lokacin da maharan suka farmusu. 

Wata majiya tace makiyayan sunyi amfani da shanu wajen dakatar da motar yan sandan ,yayin da suka bude wuta lokacin da yan sandan suka karaso domin duba abin da yatsare musu hanya. 

Jami’i daya ya rasa ransa a wurin,wani kuma ya rasu a kan hanyar kai shi asibiti.

Ragowar mutum biyu sun mutu ne a ranar Laraba, yayin da suke karbar magani a asibiti.

Wani dan sanda yace harsashi yayi kaca-kaca da motar da yan sandan ke ciki. 

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Andrew Aniamaka , ya tabbatar da faruwar harin amma yace dan sanda daya ne yarasa ransa. 

“An kaiwa mutanen mu hari,kuma insifeta daya ne ya rasa ransa,”yace 

“Sauran jami’an suna asibiti da bazan iya bayyanawa wa Jama’a ba saboda dalilan tsaro, suna murmurewa.

“muna nan muna bin sawun maharan da zarar mun kama su, zamuji dalilin da yasa suka kaiwa yan sandan mu harin kwanton bauna.”

Harin na zuwane sa’o’i 24 bayan wani dan sanda Usman Ndababo, mai mukamin Mataimakin kwamishina ya rasa ransa a wani harin bindiga.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like