Yan sanda kama wani mutum da gawar yaro kunshe a cikin buhun leda


Wani fasinjar motar haya mai suna Ajiboye Emmanuel rundunar yan sanda ta jihar Ogun suka kama bayan da aka same shi da gawar wani jariri a cikin leda da ake zargin za ayi tsafi da shi.

Mai magana da yawun rundunar Abimbola Oyeyemi wanda ya tabbatar da haka ga manema labarai ya ce mutumin da ake zargi ya ƙunshe gawar cikin wata leda.

Ya kara da cewa mutumin mai shekaru 42 ya shiga mota ne a garejin Sapade dake yankin Remo a jihar a ranar 22 ga watan Disamba tare da buhun leda da yake ɗauke da shi.

Mista Oyeyemi yace wari da doyi da yake tashi daga buhun shi ya jawo shakku a zukatan mutanen dake cikin inda suka nemi a tsaya kuma suka sanar da jami’an yan’sanda dake ofishin yan’sanda na Isara.

“Bayan samun bayanin jami’in yan’sanda na Isara, Taiwo Yusuf ya jagoranci yan’sanda zuwa gurin inda aka kama mutumin da ake zargi,”yace.

Mai magana da yawun rundunar yace bayan an duba buhun ledar ne aka gano cewa gawar yaro ce kunshe a ciki.

” Da ake masa tambayoyi mutumin da ake zargi da aikata  laifin  ya yi ikirarin cewa ya fito ne daga Offa na jihar Kwara kuma yana kan hanyarsa ta zuwa Lagos inda zai binne yaron.”

You may also like