‘Yan Sanda A Kano Sun Maka Wasu ‘Yan Shi’a A Kotu


 

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da gurfanar da wasu ‘yan Shi’a a gaban kotu bisa zarginsu da hada baki wajen aikata laifi.

Rundunar ‘yan sandan ta jihar Kano ta bakin kakakinta DSP Magaji Musa Majiya ya bayyana cewar ‘yan Shi’ar guda saba’in da bakwai na cikin wadanda suka yi tatattaki a ranar Talata, sabanin umarnin da gwamnati ta bayar cewa ta hana tare da haramta dukkannin taro ko kuma gangami da sunan addini, abunda rundunar ta ce ba zai yiwu ba wadansu ‘yan tsiraru su dinga nuna sunfi karfin doka.

Sai dai wata sabuwa wai inji ‘yan caca, ‘yan shi’ar da ake tuhuma sun musanta aikata laifin da rundunar ‘yan sandan ta ke tuhumarsu da aikatawa inda suka ce ai babu wani laifi da suka aikata da ta kai ga a yi musu irin wannan.

Daga nan sai kotu ta dage zaman zuwa ranar 18 ga watan Nuwamba mai zuwa domin a dawo kotu a fara sauraren shaidu.

Tattakin da suka yi dai ya janyo takaddama tsakaninsu da mutanen gari, lamarin da ya janyo rigima har da kone-kone.

You may also like