Yan Sanda Na Binciken Yadda Aka KasheWani Mutum Kan Laifin Satar Doya 


Rundunar yan sandan jihar Enugu ta fara bincike kan zargin da ake na kisan wani mutum bayan da aka same shi da laifin satar doya a yankin Amorji Nike dake jihar.

Mai magana da yawun rundunar, SP  Ebere Amaraizu, ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar inda yace lamarin ya faru ne ranar 4 ga watan Oktoba.

Amaraizu yace lamarin ya faru ne a cikin al’ummar Amorji Nike dake karamar hukumar Enugu ta Gabas dake jihar.

” An gano cewa wani mutum wanda har yanzu ba a gane waye ba ana zargin an dake shi har takai ya rasa ransa ranar 4 ga watan Oktoba a Amorji Nike sakamakon samunsa da laifin satar doya.

” An jefar da gawarsa a wani fili inda anan yan sanda suka gano ta,”Amaraizu yace.

A cewar sa tuni aka fara bincike yayin da aka kama mutane biyu da ake zargi da hannu kan lamarin.

“Mutane biyun da aka kama suna taimakawa yan sanda a binciken da suke,” yace.

You may also like