‘Yan Sanda Sun Cafke Matan Aure Guda 3 a Kano a Bisa Zargin Yunkurin Kisan Kai


 

 

Rundunar ‘yan sandan jahar Kano ta cafke wasu matan aure guda 3 a bisa zargin da ake musu na yunkurin kisan wata yarinya a kauyen Gayawa da ke karamar hukumar Ungoggo a Kano. ‘Yan sandan na zargin matan ne da barin yarinyar ta mutu bayan da suka wurga ta cikin rijiya.

Kakakin rundunar DSP Magaji Majiya, ya tabbatarwa manema labarai faruwar wannan al’amarin a ranar Talatar da ta gabata.

Rahotanni sun nuna cewa yarinyar wacce ta shafe kwanaki 2 a cikin rijiyar ta shiga tarko ne irin na muguwar kishiyar uwa.

Majiya ya bayyana cewa wadanda ake zargin sun aikata laifin ne a makon jiya, kuma an kama su ne a ranar Lahadin da ta gabata bayan da uban yarinyar ya kai kara.

 

Kwamishinan ‘yan sanda na jahar Rabiu Yusuf ya bayarda umarnin a mika masu laifin ga bangaren bincike akan manyan laifuka domin a yi kyakkyawan bincike akan rawar da kowannensu ya taka a laifin.

You may also like