‘Yan Sanda Sun Cafke Mutane Dauke Da Muggan Makamai A Wajen Taron PDP A JigawaRundunnar ‘yan sanda a jihar Jigawa ta cafke ayarin matasa su 132 dauke da muggan makamai jiya Lahadi a garin Bamaina dake jihar Jigawa. 
Bamaina dai shine garin tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido, kuma jiya Lahadi shi tsohon Gwamnan na Jigawa yake taro mabiya jam’iyar PDP. 
Har yanzu hukumar ‘yan sandan ba ta ce komai ba domin a cewarsu suna kan bicike, kuma da zarar sun kammala bincike za su yi wa ‘yan jarida cikakken bayani kuma daga bisani su gurfanar da su a kotu.
Makaman da aka samu a wurinsu sun hada da bindiga kirar gida daharsashi da wukake, adduna, kwari da baka.

You may also like