Rahotanni sun tabbatar da cewa rundunar ‘yan sanda ta cafke dan Majalisar Dattawan nan daga jihar Bayelsa. Sanata Ovie Agege bisa zargin daukar nauyin ‘yan dabar da suka sace sandar ikon majalisar Dattawa a yau Laraba.
Sai dai kuma majalisar tana ci gaba da zama da wata sandar, bayan sace ainihin ta majalisar da wasu ‘yan daba suka yi.Sannan majalisar ta umarci Sipeto Janar na ‘yan sandan kasar da Darakta janar na DSS da su nemo sandar, sannan su kamo wadanda suka sace ta cikin sa’oi 24.