Yan Sanda Sun Ceto Wata Mata Da Aka Sace A Jihar Cross RiverYan sanda sun ce to wata mata mai suna, Comfort Udoenwang wacce aka sace ta ranar 2 ga watan Oktoba a Jihar Cross River.

Kwamishinan yan sandan jihar,Hafiz Inuwa ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa NAN cewa an ceto matar.  ne  da safiyar yau Asabar.

Inuwa ya bayyana cewa an sace matar ne a gidanta dake karamar hukumar Calabar ta kudu inda aka kai ta kauyen Okoyong dake karamar hukumar Odukpani.

Kwamishinan yace yace sabon bangaren rundunar yan sandan jihar da aka kafa domin yaki da kungiyoyin asiri da kuma masu yin garkuwa da mutane sune suka samu nasarar ceto matar.

” Da safiyar yau ne mutane na suka dirarwa maboyar masu garkuwa da mutanen da suka kware wajen fashi da makami da kuma aikata miyagun laifuka,”yace.

“Da suka hangi jami’an tsaro bata garin sai suka bude wuta sakamakon musayar wutar ne aka kashe wani mutum daya da daga cikinsu mai suna, Isaac Sebesatan.

” An ajiye gawarsa a dakin ajiye gawa a  Asibitin Koyarwa na Jami’ar Calabar.

“Mun samu nasarar samun bindiga kirar gida, guda daya, kunshin harsashi, kakin sojin Najeriya,da kuma abin rufe fuska da kuma tutar kungiyar asiri.

“Mun samu nasarar kama daya daga cikinsu mai suna, Elle David, yayin da jagoransu Ayi Etok ya tsallake rijiya da baya amma da harbin bindiga.”

You may also like