‘Yan Sanda Sun Dakile Wani Hari A Zamfara Tare Da Kashen ‘Yan Fashin Daji Biyu
A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, CSP Mohammed Shehu, ya fitar a ranar Lahadi, Yusuf ya kuma yi kira ga jam’a da su tashi tsaye tare da ci gaba da hadin gwiwa da hukumomin tsaro a kokarinsu na maido da dawwamamman zaman lafiya da tsaro a jihar.

Sanarwar ta kara da cewa, “kwamishin nan ‘yan sandan ya yi wannan yabon ne, biyo bayan nasarar da aka samu a yayin wata kazamar arangama da wasu da ake zargi ‘yan fashin daji a wani gari a Karamar Hukumar Tsafe, inda aka dakile yunkurin kai hari da yan fashin daji suka yi kokarin kai wa, sannan aka kashe biyu daga cikinsu yayin da saura suka gudu da raunin bindiga.”

Kwamishin ‘yan sandan ya sake tabbatarwa da jama’a da ci gaba da jajircewar ‘yan sanda a yakin da ake yi da sake bullar ayyukan ‘yan fashin daji a jihar.

Ya kuma bukaci al’ummar yankunan da su hada kai da dukkanin hukumomin tsaro a jihar domin samun nasara a ayyukansu a fadin jihar.

Jihar Zamfara dai tana fama da matsalar sace-sacen jama’a da na dabbobi inda aka dan samu lafawa lamarin bayan da hukumomi suka sake yunkurowa domin magance matsalar da taki-ci-taki cinyewa.Source link


Like it? Share with your friends!

1

You may also like