‘Yan Sanda Sun Dau alwashin Hukunta Duk Masu Hannu A Rikicin Jihar KanoRundunar yansandan jihar Kano ta tabbatarwa al‘ummar jihar zata hukunta duk wanda yake da hannu a rikicin bayan hawan daushe da wasu magoya bayan yan siyasa biyu suka yi a ranar Asabar.

Kakakin rundunar yansandan jihar Kano, Dsp Majia ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya bayyana cewa jami‘an yansanda sun taimaka sosai wajen kawo karshen rigimar, ba tare da sun bari an samu asarar rayuka ba.

Ya kara da cewa jami‘an yansanda da kansu suka yi ta kokarin daukar wadanda suka samu raunuka domin kai su asibiti dan a basu kulawa.

Ya zuwa babu  asarar rayuka a rikicin, kuma babu wanda aka kama amma ana cigaba da bincike kuma duk wanda aka kama daga kowane bangare da su kansu bagaren yansanda a hannu a aikata wannan laifi za‘a hukuntasu.

Dsp Majia, ya kara da cewa, Kwamashinan yansandan jihar Kano, Rabiu Yusif yayi alkawarin yin adalci da hukunta duk wanda aka samu da laifi ko waye ko menene matsayin sa.

Kwamshinan yace ba zai yuwu ba a kokarin su na dakile harkar fadan daba a fadin jihar Kano ba wasu tsurari su kawo musu cikas ba dole sai hukunta duk wanda aka samu da laifi.

Ya kara da cewa sam bai ji dadin irin wannan abu da ya faru ba, kasancewar a irin wannan rana da alumma suke farinciki hakan ta faru babban abin takaici ne.

Kamar yadda Kakakin rundunar Dsp Majia ya bayyanawa ‘yan jaridu, yace Kwamashina ya bada umarnin gaggawa na kafa kwamitin bincike daga yau din nan domin ganin an zakulo duk wanda yake da hannu a fadan da ya faru a Hawan Daushe na ranar Asabar.

You may also like