Rahotanni sun nuna cewa ‘Yan sanda sun fara kama yan shi’ar da suka yi kunnen kashi a kan hana su fitowa zagayen da hukumar ‘yan sanda ta yi a jiya.
Duk da cewa majiyarmu ba ta tabbatar mana da jihar da lamarin ya auku ba, amma dokar dai an kafa ta ne a jihohin Kano, Kaduna da Katsina.