Yan Sanda Sun Gano Bindigogi 5 A hannun Wani Da Ake Zargi Da Aikata fashi


Hakkin mallakar Hoto: jaridar Daily Trust

Yan Sanda sun kama wani matashi Micheal Olowu dan shekara 25 da ake zargi da aikata fashi da makami a kauyen  Kabusa dake Abuja. 

Da yake gabatar da mai laifin a Caji Ofis din yan sanda dake Apo jiya Juma’a, kwamishinan yan sandan birnin tarayya Abuja, Musa Kimo yace an kama mai laifin ne a ranar Laraba da karfe 3:00 na dare.

Yace mutumin da ake zargi da kuma wasu mutane biyar wadanda ake nema ruwa ajallo, sun kai hari gidan Mista Olayinla Ayeni dake kauyen. 

Ya kara da cewa mutumin da ake zargin ya amince da aikata laifin, kana ya bayyana cewa sun kasance  cikin wata kungiyar yan fashi da makami da suke addabar kauyen na Kabusa da kewayensa.

Kayan da aka samu daga mai laifin sun hada da  bindigogi kirar gida guda 5, harsashi ,wayar hannu sanfurin Tecno, Kwamfuta Laptop guda biyu da kuma kudi  naira N35,000.

Kwamishinan yan sandan ya kuma gabatar da wasu masu laifi su hudu da aka kama da laifin satar wayar wutar lantarki. 

Ya bayyana sunayensu da suka hada  da Jonathan Duru, Chinedu Okafor, Uchenna Eke da kuma Ifeanyi Nnaji, wadanda yace dukansu suna zaune a kauyen  Mpape.

Yace an kama masu laifin da misalin karfe 4:45 na dare bayan da rundunar ta samu bayani akansu. 

You may also like