Yan sanda sun gano gawarwakin mutane 10 a jihar Benue 


Rundunar yan sandan jihar Benue ta gano  gawarwaki wasu mutanen kauye su 10  da ake zargin barayi da kashewa a kauyukan Tse-Audu da kuma Enger dake karamar hukumar Gwer ta jihar.

A wata sanarwa ranar Juma’a, a Makurdi, mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, ASP Moses Yamu,ya ce gawarwakin mutanen da aka kashe ne a harin da aka kai ranar Alhamis akan kauyukan.

Ya ce jami’an yan sandan kwantar da tarzoma da aka tura garin Naka hedikwatar karamar hukumar, su ne suka gano gawarwakin mutanen.

Ya alakanta kisan kan barayi masu ɗauke da makamai.

“Gawarwakin mutane 8 aka gano a dazukan dake kusa da kauyukan Tse-Audu da kuma Enger a karamar hukumar Gwer ta yamma.

“Wannan kari ne kan wasu gawarwaki biyu da aka samu a dai yankin a dai wannan rana.”

You may also like