Yan Sanda Sun Harbe Jami’ai Biyu Na Hukumar Kiyaye Hadura Ta Kasa  A Jihar Abia  Hukumar kiyaye afkuwar hadura ta kasa FRSC, ta tabbatar da harbin jami’anta biyu dake bakin aiki a jihar Abia.

Tun farko dai wani shaida da ya ganewa idonsa abinda yafaru ya fadawa kamfanin dillancin labarai na kasa NAN,cewa jami’an yan sanda dake kula da wani kusa a jihar sune suka harbe mutanen biyu. 

Anyi ittifakin cewa wadanda suka harbe jami’an hukumar kiyaye haduran, yan sanda ne masu tsaron lafiyar kakakin majalisar jihar Abia, Chikwendu Kanu. 

Jami’in dake kula da wayar da kan jama’a  a hukumar Bisi Kazeem, wanda ya tabbatarwa da NAN harbin mutanen, yayi shiru kan sunayen jami’an da abin ya rutsa dasu. 

Kazeem ya ce tuni aka kaiwa rundunar yan sanda rahoton faruwa lamarin domin bincike yayin da jami’an suke karbar magani a wani asibiti da ba a bayyana ba. 

” Gaskiya ne an harbin jami’an mu da yamman nan,ankai rahoton faruwar abin ga hukumomin yan sanda yanzu haka muna jiran rahoton bincikensu. 

 ” ma’aikatan da suka samu rauni an kwantar dasu a asibiti kuma suna samun sauki.

” Wannan bazai tsorata jami’an mu ba wajen gudanar da aikinsu a maimakon haka ma zai kara musu kwarin gwiwar  kare hanyoyin mu,”yace.

 A cewa NAN lamarin yafaru ne a mahadar Umuikea a karamar Hukumar Isiala Ngwa ta Kudu. 

Wadanda suka ganewa idonsu abinda yafaru sun ce motar sintiri ta FRSC ce ta dakatar da wata mota dake dauke da matar shugaban majalisar  kan rashin amfani da bel na kujera.

“Mata uku ne a cikin motar kuma dukansu basu saka bel din ba.  

” Yayin da jami’an kiyaye haduran suka fara yi musu magana nan danan suka harzuka suka fara yiwa jami’an fada. 

“Matar kakakin majalisar ce ta dau waya takira jami’an tsaron mijinta inda suka bayyana a wurin cikin mintuna kadan, aikuwa  da zuwansu suka shiga harbin kan me uwa da wabi. 

 “Yayin da suke harbin ne aka samu daya daga cikin jami’in kiyaye haduran a hannun yayin dayan aka same shi a wuya da kuma kugunsa. ” 

You may also like