Yan Sanda sun harbe mutane 192 dake mu’amala da miyagun kwayoyi


 

Yaki da masu safarar miyagun kwayoyin da sabon shugaban kasar Philippines Rodrigo Duterte ya kaddamar yayi sanadiyar kashe mutane kusan 200, abinda kungiyoyin kare hakkin Bil Adama ke adawa da shi.

Mai Magana da yawun fadar shugaban kasar Martin Andanar yace suna samun gagarumar nasara, yayin da wasu daga cikin al’ummar kasar ke yabawa matakin ganin irin illar da kwayoyin ke haifar musu.

Rahotanni sun ce a cikin watanni 2, ‘Yan Sanda sun harbe mutane 192 dake mu’amala da kwayoyi kamar yadda shugaban kasar ya basu umarni.

Tun a lokacin yakin neman zaben sa ne, shugaba Duterte yace akalla mutane 100,000 yake saran zasu mutu wajen yaki da masu safarar kwayoyin, kuma za’a sanya gawawakin ruwa dan kifi su ci suyi kiba.

Gwamnatin kasar Philippines dai ta yaba da yakin da ta kaddamar da masu safarar kwayoyi wanda yanzu haka ya lakume rayukan mutane kusan 200 duk da sukar da suke fuskanta na take hakkin bil’adama.

You may also like