Jami’an tsaron ‘yan sanda sun kai samame tare da cafke wasu daga cikin matasan da suka kwana suna gwafza fada a shiyoyin Binanchi da iraki kake jihar sakkwoto.
Tun cikin daren jiya Alhamis ne jami’an suka fara kai samame a dukkanin bangarorin biyu inda suka samu nasarar cafke fiye da mutane ashirin da biyar daga dukkanin bangarorin.
Yanzu haka dai jami’ai na cigaba da sintiri a fadin shiyoyin.
Wannan dai wani mataki ne da hukumar ta dauka da zimmar takaita tashin hankalin dake tsakanin shiyoyin biyu, hakan ya faru ne saka makon dogayin muryoyin da jama’a suka rinka yi domin ganin an kai karshen wannan matsala.