‘Yan Sanda Sun Kai Sumame Gidan Dame Patience Jonathan 


Patience Jonathan

Rahotanni sun tabbatar da cewa ‘yan sanda sun ka wani samame gidan Uwargidan tsohon Shugaban kasa, Misis Patience Jonathan da ke yankin Maitama a Babban Birnin Tarayya Abuja.

Wata majiya ta nuna cewa Misis Patience ta sayi gidan ne don bayar da shi kyauta ga kaninta. Hukumar EFCC dai na ci gaba da matsa bincike kan Uwargidan shugaban kasa inda kwanaki a rufe asusun ajiyarta da ke bankuna guda biyar wadanda ke kunshe da kudade har sama da Naira Bilyan Tara.

You may also like