Yan sanda a jihar Adamawa sun kama, Abel Bchora, mai neman tsayawa takarar gwamna a karkashin jam’iyyar SDP bisa zargin yin kalaman tayar da hankali.
Othman Abubakar, kakakin rundunar yan sandan jihar shine ya tabbatarwa da yan jaridu kamen, ranar Litinin a Yola babban birnin jihar.
Mai magana da yawun rundunar ya ce Bichora ya aikata laifin a wata hira da aka yi da shi ta kai tsaye a gidan wani rediyo mai zaman kansa dake Yola.
Abubakar ya ce za a gurfanar da Bichora gaban kotu bisa tuhume-tuhume guda hudu da suka hada da bata suna da kuma fadawa jama’a maganganun karya akan yan sanda.
Ya shawarci yan siyasa da su gudanar da siyasa kamar yadda doka ta gindaya ya kara da cewa yan sanda a shirye suke su tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a jihar.