Rundunar yansandan jihar Kaduna ta kama masu aikata laifi 36, tare da kwato dabbobi 426 daga hannun barayin shanu a Kaduna.
Kwamishinan yansandan jihar Agyole Abe, ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai, yace mutanen sun aikata laifuka daban-daban da suka hada da aikata Fyade, fashi da makami, sayar da miyagun kwayoyi,satar man fetur,Luwadi, garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuka.
Yace “abubuwan da aka kwato daga barayin shanun sun hada da dabbobi 420,wadanda aka damka su ga gwamnati karkashin rundunar tsaro ta musamman da ake kira ‘Operation Yaki’domin mayar dasu ga mamallakansu.”
“Mun gano bindigogi guda 7 kirar gida sanfurin AK-47,karamar bindiga kirar gida da kuma harsashi,buhunan ganyen tabar wiwi 7.”
Kan batun yan sara- suka da suka addabi jihar kwamishinan yace tuni rundunar ta kama shugaban tsagerun na jihar.
Da yake magana kan rikicin kudancin Kaduna Agyale,yace “An shawo kan rikicin da yake addabar kudancin jihar sakamakon tattunawa da al’umomin yankin suke. “