‘Yan Sanda Sun Kama Tirela Dauke Da Makaman Kungiyar Shi’a A Jihar Kano


Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ta kama wata babbar mota dauke da makaman `yan kungiyar Shi’a. 

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, Magaji Musa Majiya ya shaida wa manema labarai ranar Juma’a cewa motar tirelar tana kan hanyarta ne daga Yobe zuwa Zaria. Sai dai sashin Hausa na BBC ya yi kokarin jin martanin ‘yan Shi’ar bisa wannan batu amma hakan bai bai yi nasara ba.

You may also like