Jami’an yan sanda sun kama Abdullahi Krishi wakilin jaridar Daily Trust a majalisar wakilai ta tarayya.
Yan sandan dake majalisar wakilai, su ne suka dira cibiyar yan jaridu dake harabar majalijsar karkashin jagorancin Dele Olaoye inda suka nemi ganin Krishi.
Olaoye daga bisani ya mika danjaridar ga wasu jami’an tsaro inda suka saka shi cikin w wata mota kirar Hilux suka kuma yi awon gaba da shi.
Babu wasu bayanai da ke nuna dalilan da yasa aka kama shi sai da wasu rahotanni na cewa gwamnan Jigawa Muhammad Badaru Abubakar na da hannu a kama shi da aka yi.
Kama Krishi da akayi na zuwa ne mako guda bayan da jami’an hukumar tsaro ta farin kaya sun kama Tony Ezimakor wani dan jarida dake aiki da jaridar Independent kan wani labari da ya rubuta.