Yan sanda sun kama wani mutum da takalman sata kafa 13


An kama wani mutum da takalma kafa 13 da ake zargin sato su yayi daga wani shagon sayar da kayan sawa a Gwarinpa dake Abuja.

Wata majiyar yan sanda ta ce an kama mai laifin mai laifin ranar Alhamis da takalman da darajarsu ta kai ₦795,000.

” Takalman iri daban-daban ne yan kasashen da waje,” majiyar tace.

Mutumin da ake zargin mai suna Tukur ya amince da aikata laifin fasa shagon sayar da kayan inda ya saci takalman.

Baturen yan sanda na Gwarinpa CSP Nuruddeen Sabo ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce mutumin da ake zargi ya fada komar jami’an tsaro da suke gudanar da sintiri da karfe 3:00 na dare.

You may also like