Yan Sanda Sun Kama Wani Mutum Dauke Da Kan Mace Sabon Yanka


Rundunar yan sandar jihar Osun ta kama wani mutum mai shekaru 38, Ajibade Rashid, dauke da kan mutum sabon yanka a birnin Osogbo,babban birnin jihar.

Da yake nuna mutumin ga manema labarai Kwamishinan yansandan jihar,Mista Fimihan Adeoye, yace yansanda sun kama Ajibade a yankin Olu-ade.

Kan mace sabon yanka, hanta, hanji, huhu,matucin matar da kuma wata  roba cike da jini, sune abubuwan da aka gano a hannun mutumin da ake zargi.

Kwamishinan yace an fara bincike domin gano matar da yake dauke da kanta, yakara da cewa za’ayi cikakken bincike tare da hukunta duk wanda ke da hannu. 

You may also like