Yan sanda sun kama wasu masu garkuwa da mutane dake sanye da kakin soja


Rundunar yan sandan jihar Osun ta kama wasu masu garkuwa da mutane su uku da suka hada da Henry Omenihu,Paul Chituru da kuma Henry Bright wadanda suke gudanar da muguwar sana’ar tasu sanye da kakin soja.

Kwamishinan yan sandan jihar Osun,Fimihan Adeoye, ya yi baje kolin mutanen uku ga manema labarai a hedikwatar rundunar dake Osogbo babban birnin jihar Osun.

Kwamishinan ya ce mutanen da ake zargi sun yi garkuwa da Mista Kayode Agbeyangi da Uwargida Oyeyemi Obafemi akan babbar hanyar Ilesa zuwa Ibadan a ranar 14 ga watan Afirilu shekarar 2018

Ya ce mutanen biyu suna tafiya ne akan babbar hanya lokacin da wadanda ake zargin suka harbi tayar motar su kirar Toyota Camry sakamakon haka ya sa suka tsaya inda mutanen sanye da kayan sojoji suka tilasta musu fitowa daga ciki.

Bayan sun yi garkuwa da mutanen na tsawon kwanaki hudu a karshe sun samu nasarar karɓar kudin fansa har naira miliyan biyu daga yan uwansu kafin daga bisani su sake su.

Kwamishina Adeoye, ya kara da cewa mutanen da ake zargin sun karbi kudin fansar ne a jihar Rivers.

An samu bindiga guda daya kirar Ak-47 da kuma kakin soja guda hudu.

You may also like