Yan Sanda Sun Kama Yan Uwa Biyu Da Laifin Fashi Da Makami Sun Kuma Kwato Motar Da Suka Sata


Rundunar yan sandan birnin tarayya Abuja ta kama  wasu yan uwa biyu da laifin fashi da makami inda ta samu wata mota da aka sace a hannunsu.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar yan sandan birnin,Anjuguri manza, yafitar yace  shugabar caji ofis din yan sanda na Asokoro, CSP Aisha Yusif,ta shaidawa kwamishinan yan sandan birnin,Musa Kimo,  kama mutanen da akayi.
Ya bayyana sunan mutanen da ake zargi da aikata laifin da suna  Solomon Manger, da kuma Isaac Manger, wanda ya bayyana su a matsayin wa da kani da suka fito daga karamar hukumar kwande ta jihar Benue.

  Mutanen biyu  da ake zargi sun kware wajen kwace mota a hannun masu sana’ar  tasi,yan sandan dake aiki a caji ofis na Asokoro ne suka kama mutanen a ranar Alhamis da misalin karfe 9:20 na dare.

Yace an kama mutanen ne bayan da aka samu rahoton cewa sun kwace wata mota kirar Honda.

Sanarwar ta kara da cewa  masu laifin suna gudanar da mummunan sana’arsu tsakanin Wuse da kuma kauyen Kurunduma ta wajen gadar dake barikin sojoji na Mogadishu an kama sune lokacin da suke kokarin kwace wata mota daga hannun direban tasi da suka shiga daga Wuse Zone 2.  

You may also like