Yan sanda sun rufe sakatariyar jam’iyar APC reshen jihar Ekiti


Rikicin da yake addabar jam’iyar APC reshen jihar Ekiti ya dauki wani sabon salo a ranar Litinin bayan da yan sanda suka rufe ginin sakatariyar jam’iyar.

Masu zanga-zanga dake goyon bayan tsohon gwamnan jihar kuma ministan ma’adanai,Kayode Fayemi sune suka mamaye ginin sakatariyar jam’iyar dake kan titin Ajilosun- Ikere inda suka bada sanarwar sauke shugabannin jam’iyyar karkashin jagorancin, Jide Awe.

Masu zanga-zangar sun kuma bada sanarwar kafa kwamitin riko dake kunshe da masu goyon Fayemi.

Amma kuma yan sanda dauke da makamai sun isa sakatariyar inda suka umarci kowa ya fice kafin su rufe ofishin.

Masu zanga-zangar sun ce sun je sakatariyar ne domin su nuna rashin goyon bayansu kan halayyar shugabannin jam’iyar.

Rikicin dake addabar jam’iyar ya samo asalin daga wurin zaben fidda gwani na dan takarar gwamnan jihar.

An dai tashi daga zaben baram-baram ba tare an kammala shi ba.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like