‘Yan Sanda Sun Tarwatsa Bikin ‘Yan Kwankwasiyya A KanoRundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tarwatsa wani bikin karrama daliban da tsohon Gwamnan jihar, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya dauki nauyin karatunsu zuwa kasashen waje wanda mabiya tafiyar Kwankwasiyya suka gudanar a Cibiyar Binciken Tsarin dimokradiyya na Aminu Kano da ke Mambayya.
Da yake nuna takaicinsa kan matakin ‘yan sandan, Shugaban Bangare na APC na jihar, Alhaji Umar Haruna Doguwa ya bayyana cewa kotun koli ta fayyace batun neman Izinin gudanar da taro wanda kuma kungiyar ta bi wannan mataki amma kuma jami’an tsaron suka tarwatsa su. Ya kara da cewa babu wanda ya isa ya hana su bin akidarsu ta Kwankwasiyya.

You may also like