‘Yan Sanda Za Su Gudanar Da Bincike Kan Zargin Rashawa Da Ake Wa Shugaba Zuma


4bk85b6dc3117dcpw4_800c450

 

Babbar jam’iyyar ‘yan adawa ta kasar Afirka Ta Kudu, Democratic Alliance (DA) ta sanar da cewa ‘yan sandan kasar sun sha alwashin gudanar da bincike dangane da zargin rashawa da cin hanci da ake yi wa shugaban kasar Jacob Zuma.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewar Jam’iyyar Democratic Alliance (DA) ita ce ta shigar da wannan karar a makon da ya wuce bayan da hukumar da ke fada da rashawa da cin hanci na kasar Afirka ta Kudun ta fitar da wani rahoto da ke nuna cewa akwai zarge-zargen da ake yi wa jami’an gwamnatin shugaba Jacob Zuman.

Cikin wata sanarwa da ya fitar, shugaban jam’iyyar ta DA Mmusi Maimane ya ce ‘yan sandan da ke binciken manyan laifuffuka ciki kuwa har da rashawa da cin hanci a kasar Afirka ta Kudun da ake kira da Hawks za su gudanar da bincike kan zargin da ‘yan adawan suke wa shugaba Zuma da rashawa da cin hanci.

A ranar 2 ga watan Nuwamban nan ne hukumar da ke fada da rashawa da cin hanci na kasar Afirka ta Kudu ta fitar da wani rahoto dangane da zargin rashawa da cin hanci da ake yi wa shugaba Zuman da wasu ministoci da mukarrabansa.

You may also like