‘Yan sanda za su gurfanar da Dino Melaye da wasu mutane hudu a gaban kotu ranar 10 ga watan Mayu


Rundunar Yansandan Najeriya, ta ce zata gurfanar da sanata Dino Melaye a gaban kotu da kuma sauran mutane hudu da aka sake kamawa.

Za a gurfanar da sanatan da kuma mutanen hudu a  gaban Babbar Kotun Tarayya dake Lokoja,ranar 10 ga watan Mayu bisa zargin hada baki wajen mallakar makami ba bisa ka’ida ba.

Mutanen da ake zargi su ne: Kabiru  Seidu mai shekaru 31 da akafi sani da suna Osama, Nuhu Ilias da ake kira Small, Musa Muhammad mai shekaru 27 da aka fi sani da suna Iko da kuma Emmanuel Audu mai shekaru, 26.

 Kafafen yada labarai da dama dake kasarnan sun ruwaito cewa a ranar 28 ga watan Mayu rundunar yan sandan jihar ta bada sanarwar tserewar wasu batagari daga caji ofis na yan sanda ciki har da Seidu da Salisu.

Har ila yau a ranar 30 ga watan Maris rundunar Usamatu a ba da sanarwar sake kama hudu daga cikin mutanensa da suka tsere.

Mai magana da yawun rundunar, Jimoh Moshood shine ya bayyana haka lokacin da yakewa manema labarai jawabi kan sake kama mutanen hudun da yansanda su ka yi ,ya ce biyu daga cikin mutanen da ake zargi har yanzu ba a san inda suke ba.

You may also like